Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tasirin hana achaba a Kano

Image caption Dama can akwai dokar takaita zirga-zirgan babura a jihar ta Kano

A karshen watan Janairun bana ne gwamnatin jihar Kano ta hana daukar mutane a kan babura a kananan hukumomi tara na cikin birni.

Abin da hakan ya haramta sana'ar acaba a birnin na Kano da dubban mutane ke amfani da shi a matsayin hanyar sufuri.

Hana hawa baburan dai ya janyo wahalar samun abubuwan hawa na haya, inda jama'a kan shafe lokuta suna jiran abubuwan hawa.

Gwamnatin ta Kano dai ta ce ta dauki wannan mataki ne, saboda dalilai na tsaro, inda kuma ta umarci masu baburan da su yi rijista dan tantance su.

Matakin na hana daukar mutane a bubura, da kuma haramta zurga-zurgarsa bayan karfe shida na yamma, ya sa kasuwar masu kekuna ta bude.

A kan haka ne wakilin mu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya hada mana rahoto na musamman: