Masu zabe a Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Hadewar sabuwar PDP da APC

Image caption Masu zabe a Najeriya

A farkon wannan makon ne gwamnoni biyar daga cikin bakwai na sabuwar PDP da suka balle daga uwar jam'iyyar PDP, kuma suka bada sanarwar hadewa da babbar jam'iyyar adawa ta APC.

Gwamnonin biyar sun ce, suna dau wannan mataki ne domin a sami sauyi a fagen siyasar kasar.

To anya kuwa kwalliya za ta biya kudin sabulu? Kuma ko yaya sabon kawancen zai kasance?