Shugaba Jonathan na Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar gidaje a Najeriya

Image caption Gidajen a Najeriya

Hukumomin Nijeriya sun kaddamar da wani kampani da zai taimaka a yunkurin samar da gidaje ga jama'a a Nijeriya.

Matsalar gidajen na daga cikin matsalolin dake ci ma jama'a tuwo a kwarya, rahotanni na nuna cewa akwai gibin gidaje akalla miliyan sha bakwai a Nijeriya.

Ga wadanda ke zaune a gidajen ma ana cewa wasu gidajen bai kamata ce mutane na zaune a cikinsu ba.

Shin me ya janyo matsalar karancin gidajen, kuma ta yaya za a shawo kanta?

Wasu kenan daga cikin abubuwan da zamu tattauna kan su a filinmu na Ra'ayi Riga.