Janar Buhari na APC da Shugaba Jonathan na PDP
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Manufofin yakin neman zabe

Hakkin mallakar hoto AFP AP
Image caption 'Yan takarar Shugabancin Najeriya Janar Buhari na APC da Shugaba Jonathan na PDP

A Najeriya yanzu haka dai yantakarar mukamai daban daban na ci gaba yakin neman zabe a ko'ina cikin kasar domin tallata hajarsu da kuma manufofin jama'iyunsu don neman amincewar masu zabe. To shin kun gamsu da irin manufofi da 'yan takarar suke yadawa a yakin neman zaben nasu, da kuma salon da suke amfani da shi wajen yadawar?