Masu kin jinin baki a Afrika ta Kudu
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Kyamar baki a Afrika ta Kudu

A 'yan makonnin da suka wuce ne dai wasu 'yan Afrika ta Kudu suka shiga kai hare hare a kan baki 'yan wasu kasashen Afrika, bisa zargin suna kwace masu ayyukan yi. Kuma wadannan hare-haren sun yi sanadin asarar rayuka da dukiya da kuma jikkatar baki da dama.

Wannan lamari dai ya haddasa zanga-zanga ta Allah wadai da hare-haren, a wasu kasashen Afrika

Shin, Yaya kuke kallon wannan matsala ta kai farmaki kan 'yan wasu kasashen da suka ba da gudunmawa wajen gwagwarmayar 'yanta Afrika ta Kudun?

Kuma wadanne matakai suka kamata a dauka wajen shawo kan matsalar?