Shugaba Macky Sall na Senegal kuma shugaban Kungiyar Ecowas
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Cikar ECOWAS shekaru arba'in

Image caption Shugaban Kungiyar Ecowas

A makon nan ne aka yi bukin cika Shekaru 40 da kafa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma -ECOWAS ko CEDEAO. Su dai jami'an kungiyar suna cewar ta taka rawar gani cikin shekarun musamman fannin zaman lafiya da kyautata mulkin demokuradiya. Ya kuke ganin aikace aikacen kungiyar ta ECOWAS a cikin wadannan shekaru, kwalliya na biyan kudin sabulu, kuma wadanne fannoni ya kamata a kara ingantawa a ayyukanta. Batutuwan da aka tattauna kenan a filinmu na Ra'ayi Riga!