Gidan Pirimiyan Arewa a Kaduna, Sir Ahmadu Bello
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Shekaru hamsin da juyin mulkin farko a Najeriya

Shekaru 50 kenan tun bayan juyin mulki na farko a Najeriya wanda kawo karshen Jamhuriya ta farko a kasar.

Wasu hafsoshin sojin kasa na kasar ne suka shirya juyin mulkin, a karkashin jagorancin Manjo Chukwuma Nzeogwu, da nufin kawo karshen tabarbarewar da suka ce lamuran sun yi a wancan lokacin.

Juyin mulkin dai ya haifar da sauye-sauye a tsarin siyasa da zamantakewa da kuma tattalin arziki a kasar ta Najeriya.

An kashe wasu manyan yan siyasa na kasar musamman daga arewa ci -- Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Pirimiyan yankin arewa da Sir Abubakar Tafawa Balewa, Pirayim Ministan Najeriya da kuma Samuel Ladoke Akintola, tsohon Firimiyan yammacin Naijeriyada wasu jami'an gwamnati.