Yaran makaranta a Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Bayar da ilmi kyauta a kasashen Afrika

Batun bada Ilmi wani abu ne mai muhimmanci a matsayin ginshikin ci gaban al'umma.

A kan haka ne wasu gwamnatoci suka dauki manufar bada Ilmin kyauta a wadansu matakai.

A Najeriya ma an dade ana bin tsarin bada Ilmi kyauta a kananan makarantu.

Shin ko a nahiyar Afrika za a iya bada ilmi kyauta kuma ya kasance mai inganci? Kuma wadanne matakai ya kamata a dauka domin habaka samar da ingantaccen ilmi kyauta? Ya lamarin yake a yankunanku?

Abun da muka tattauna kenan a filin Ra'ayi Riga!