Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Haramta shigo da tsoffin tayoyi Nigeria

Wannan shine lokacin da mataimakin sifeto janar na 'yan sanda mai kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, Muhammad Musa Katsina, ke karin haske akan tsofaffin tayoyi da aka shigo da su Najeriya.

Mataimakin sifeto janar ya ce an shigo da haramtattun tayoyi masu dumbin yawa da aikinsu ya kare ta haramtacciyar hanya zuwa Najeriya.

Yanzu haka dai rundunar ta ce ta fara bin shago-shago a kasar domin kwace da kona tayoyin.

A baya dai hukumar kiyaye hadururruka a Najeriya FRSC, ta ce daga watan Fabrairu zuwa Afrilun bana, bincikensu ya gano akasari daga faduwar motoci na da nasaba da irin wadannan tayoyi da aikinsu ya kare.

A yanzu dai an kama mutumin da ake zargi shi ya shigo da kwantainar tayoyin.