David Cameron
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ficewar Birtaniya da Kungiyar EU

Tuni dai sakamakon zaben raba gardamar ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai ta EU ya haddasa martani daban daban a ciki da kuma wajen Birtaniyar. Pirayim Ministan Birtaniyar David Cameron dai ya bayyana aniyarsa ta yin murabus nan da 'yan makonni, darajar kudin Burtaniya ta Fam ta fadi, hannayen Jari sun yi kasa.