Canada ta ce tana maraba da Musulmai 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Canada ta ce tana maraba da Musulmai 'yan gudun hijira

Firai ministan Canada Justin Trudeau, ya sha alwashin karbar bakuncin 'yan gudun hijira Musulmai daga kasashe bakwai da Amurka ta dauki matakin hana su shiga kasarta.

Hukumar tsaro ta cikin gida ta Amurka ta ce dokar hana shiga kasar tata za kuma ta shafi Amurkawa 'yan asalin kasashen bakwai da suka hada da Sudan da Somaliya da Yemen da Iran da Iraki da Syria da kuma Libiya.

Mista Trudeau ya bayyana matsayarsa ne a shafukan sada zumunta na zamani, inda ya ce, "a shirye muke mu bai wa wadanda yaki ya koro daga kasashensu mafaka."

A shafinsa na Twitter, Mista Trudeau ya rubuta cewa, ''Muna maraba da duk wani dan gudun hijira, ba ruwanmu da bambancin addini. Mu na kowa ne.''

Dama dai ko ministan shige da fice na Canada ma Ahmed Hussen, dan asalin kasar Somaliya ne da ya yi gudun hijira.

Wasu amsoshin tambayoyinku kan akidun Trump

An yi artabu da dan bindiga a Canada

Labarai masu alaka