Garabasa ga mai sha'awar aikin jarida da BBC

BBC London
Image caption Wannan garabasa za ta ba ku damar zuwa BBC London

BBC ta fitar da wata sabuwar dama ga masu sha'awar aikin jarida da kuma samun damar sanin yadda ake aiki a kafar yada labaran.

Wannan aiki zai baku damar yin aiki a bangare biyu na BBC, wato sashen Turanci da kuma sashe daya daga cikin harsunan da ake watsa labarai da su.

Ba a bukatar sai kana da kwarewa ko gogewa a aikin jarida, amma ana so ka zama mai sha'awar aikin.

Bugu da kari kuma, wadanda ke da izinin yin aiki a Burtaniya ne kawai za su nemi wannan aiki.

Za ku samu damar da za a horar da ku yadda ake aikin rediyo da talbijin da aikin jarida na kafafen sada zumunta na zamani a hedikwatar BBC da ke London.

Za ku samu damar kasancewa da sashen babbar kafar yada labarai ta BBC da sauran sassan kamfanin.

Aikin zai kuma ba ku damar gogayya da manema labarai da ke aiki a harsuna biyu da masu shirya shirye-shirye da editoci da masu gabatar da shiri da masu kula da kamara da masu kula da shafukan intanet da na sada zumunta.

Za ku samu damar da za ku iya gabatar da shawarwari kan wasu labarai da kuke ganin ya kamata BBC ta yi, wanda za a iya amfani da su a sassa daban-daban na ma'aikatar.

Image caption Samu damar kasancewa da BBC

Wanda zai iya nema

Domin samun damar wannan garabasa ana so ka zama gogagge a harshen Ingilishi da kuma daya daga cikin wadannan harsuna sosai da kuma rubuta su:

Hausa ko Larabci ko Azeri ko Bengali ko Burmese ko Chinese ko Dari ko Kinyarwanda ko Kirundi ko Kyrgyz ko Faransanci ko Hindi ko Indonesia ko Nepali ko Pashto ko Yaren Rasha ko Sinhala ko Somali ko Swahili ko Tamil ko Thai ko Yaren Turkiyya ko Ukrainian ko Urdu ko Uzbek ko Vietnamese.

Haka kuma mutum ya zama wanda ke da son sanin labaran duniya da abin da duniyar ke ciki.

Ana kuma so ka san yadda kafar yada labarai ta BBC ke gudanar da ayyukanta.

Ana so wanda duk zai nemi wannan aiki mace ko namiji su haura shekara 18.

Za a rufe wannan garabasar a ranar Talata 14 ga watan Fabrairu, 2017.

Maza ku garzaya wannan shafin ku samu wannan damar.

Labarai masu alaka