Tanzania: An kulle wani mai yi wa 'yan yawon bude ido tafinta

Mai kewayawa da masu yawon bude ido da mai yawon bude idon Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Mai kewayawa da masu yawon bude idon da mai yawon bude idon sun ce suna zolayar abokansu ne na shafin sada zumunta na Facebook

An kama wani mai kewayawa da masu yawon bude ido bayan ya yi fassarar ra'ayin wata mai yawon bude ido ba dai-dai ba.

Ba a bukaci Saimon Sirikwa ya nemi afuwa ba kuma 'yan sanda sun kulle shi.

Sai dai ya sake saka wani bidiyo a inda shi da matar 'yar yawon bude idon ke cewa bidiyon farko da suka nada zolaya ce kawai.

'Yan sanda sun ce a makon da ya gabata ne ma'aikatar yawon bude ido ta kasar ta kama shi saboda zargin bata mata suna da ya yi.

Mista Sirikwa dai yana aiki ne a gandun namun dajin Serengeti da ke kasar Tanzania.

A bidiyon farko da ya saka a shafin Facebook a ranar Litinin din da ta gabata, Sirikwa ya ce mai yawon bude idon ta ce 'yan kasar Tanzania suna korafi a kan yunwa.

Labarai masu alaka