FA ta tuhumi kociyan West Ham kan rashin da'a

Slaven Bilic Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Za a iya yi wa jami'an biyu hukuncin hana su zuwa bakin fili

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi kociyan West Ham Slaven Bilic da laifin rashin da'a a wasan da suka yi canjaras 2-2 da West Brom ranar Asabar.

Alkalin wasa Michael Oliver ya koro Bilic, mai shekara 48, saboda cikin fushi ya fizgi wani makurufon talabijin da ke filin ya jefara da shi kasa, saboda haushin kwallon da Gareth McAuley ya farke ana dab da tashi daga wasa.

Haka shi ma mataimakin Bilic din Nikola Jurcevic (YURCHECH), hukumar ta FA, ta tuhume shi da laifin barin iya wurin da ya kamata ya tsaya, a lokacin da ya je yana korafi kan kwallon da alkalin wasa ya hana ta Sofiane Feghouli wadda alkalin ya ce ya yi satar gida.

Kociyan da mataimakin nasa suna da dama har zuwa ranar Alhamis 16 ga watan Fabrairu, da karfe bakwai na yamma agogon Najeriya, su bayar da bahasi.

Za a iya yi wa jami'an biyu hukuncin hana su zuwa bakin fili, a lokacin wasansu, tare kuma da yi musu tara, idan an same su da laifi.

West Ham za ta yi wasanta na gaba ne a gidan Watford a gasar Premier ranar 25 ga watan Fabrairu, kafin kuma ta yi wasan hamayya na Landan a gida da Chelsea ranar 6 ga watan Maris.

Labarai masu alaka