'Mai bai wa Trump shawara kan tsaro Michael Flynn ya yi murabus kan Rasha

White House national security adviser Michael Flynn (C). Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mr Flynn yana da "cikakken goyon bayan" Shugaba Trump, in ji fadar mai magana da yawun White House Kellyanne Conway

Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan sha'anin tsaro Michael Flynn ya yi murabus bayan da rahotanni suka tabbatar cewa ya yi wata tattaunawa da jakadan Rasha a kasar tum ma kafin a rantsar da gwamnatinsu, lamarin da ya keta dokokin Amurka.

Da farko dai Mr Michael Flynn, wanda tsohon laftanar janar na sojan amurka ne, ya musanta zargin cewa ya yi wata hira da jakadan na Rasha a Amurka kan yiwuwar janye wa Rasha takunkumi gabanin hawan wannan gwamnati.

Shi kansa mataimakin shugaban kasar Mike Pense ya rika kare shi a kan wannan batu.

Sai dai a wasikar da ya rubuta ta sauka daga kan kujerarsa, Mr Flynn ya ce ya shirga wa mataimakin shugaban kasar da wasu jami'an gwamantin karya kan tattaunawar da ya yi ta waya da jakadan Rasha a Amurka.

Kafofin watsa labaran Amurka sun ce a watan ne ma'aikatar shari'ar kasar ta gargadi shugaba Trump cewa Mr Flynn ya yi tataunwar da jakadan na Rasha.

Sun ce hakan zai sa Rashar ta rika amfani da shi wajen sarayar da harkokin tsaromn Amurka.

Wata sanarwa da fadar White House ta fitar ta ce an nada Janar Joseph Keith Kellogg a matsayin mai bai wa shugaban kasar shawara a kan sha'anin tsaro na rikon-kwarya.

Tattaunwar da Mr Mr Flynn dim ya yi da jakadan na amurka tun ma kafin su hau kan mulki ta yi karan-tsaye ga dokokin Amurka, domin kuwa a wancan lokacin, shi ba jami'in gwamnati ba ne.

Da ma dai fadar Whitew House ta ce Shugaba Donald Trump "na yin duban tsanaki" kan zargin da ake yi na dangantaka tsakanin mai ba shi shawara a kan sha'anin tsaro da kuma kasar Rasha.

A ranar Litinin da maraice ne mai magana da yawun fadar White House Sean Spicer ya ce: "Shugaban kasa yana yi wa batun duba na tsakani. Yana tattaunawa da mataimakinsa da kuma wasu masu ruwa-da-tsaki kan batun domin ganin ko hakan ya yi tasiri kan tsaron kasarmu."

Mr Spicer ya yi wannan bayani ne jim kadan bayan wata babbar jami'ar fadar ta White House Kellyanne Conway ta ce Mr Flynn "yana sa ran zai samu "cikakken goyon bayan" Shugaba Trump.

Labarai masu alaka