Amurka ta sanya wa mataimakin shugaban Venezuela takunkumi

Venezuela Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tareck El Aissami ne mai ikon a Venezuela

Amurka ta kakaba takunkumi a kan sabon mataimakin shugaban Venezuela, Tareck El Aissami, bisa zargin yana da hannu a harkar fataucin miyagun kwayoyi a duniya.

Da wannan takunkumi an saka sunan Tareck El Aissami a cikin jerin hamshakan jagororin masu fataucin miyagun kwayoyi na Amurka saboda muhimmiyar rawar da ake zargin yana takawa a fataucin miyagun kwayoyi a kasashen duniya.

Shi ma attajirin nan Samark Lopez, wanda aka kwatanta shi da babban yaron Mista El Aissami, an kakaba masa takunkumin.

A watan jiya ne Shugaba Nicolas Maduro ya nada Mista El Aissami.

Mista El Aissami bai mayar da martani nan take ba amma a baya ya sha musanta zargin.

Yana da karfin fada-a-ji a cikin jam'iyyar PSUV mai mulki kuma Mista Maduro ya ba shi ikon na gudanar da wasu abubuwa wadanda a bisa al'ada shugaban kasar ke gudanarwa, wadanda suka hada da shata kasafin kudi ma'aikatu da kuma kwace iko da kamfanoni masu zaman kansu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nicolas Maduroa ya nada shi mataimakin shugaban kasar watan da ta gabata

Ma'aikatar kudi ta Amurka na zargin Mista El Aissami da taimakawa wajen safarar miyagun kwayoyi masu dimbin yawa daga Venezuela zuwa Amurka ta jiragen sama da na ruwa.

Ta kuma ce wani kasurgumin dillalin miyagun Ĉ™wayoyi a Venezuela, Walid Makled, ya taba biyan shi domin ya ba da kariya ga miyagun kwayoyin da yake fatauci.

Takunkumin ya kunshi kwace dukiyarsa a Amurka da kuma haramta masa shiga kasar.

Ma'aikatar kudi ta Amurka ta kuma sanya takunkumi a kan kamfanoni 13 a tsibiran Virgin na Birtaniya, da Panama, da Birtaniya, da Amurka, da kuma Venezuela, wadanda ke da alaka da Mista Lopez.

Mista Lopez ya musanta zargin cewa yana fataucin miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa babu wata shaida ko hujja a shari'ance ta saka sunan shi a cikin wadanda aka sanya wa takunkumi, illa alakarsa da Mista El Aissami.

Labarai masu alaka