Ma'auratan da suka yi auren dala ɗaya sun samu tagomashi

Kenyan couple
Image caption A bikinsu na farko, ma'auratan sun yi ne babu kyak da furanni gami da sauran kayan ƙyale-ƙyale

Ma'auratan Kenya da suka kashe dala ɗaya kacal a aurensu sun sake shagali a wani ƙasaitaccen bikin ranar masoya da masu fatan alheri suka ɗauki nauyi.

Labarin auren da aka kashe kuɗi mafi ƙaranci cikin watan jiya ya kankane shafukan sada zumunta, inda 'yan Kenya da dama suka yi tayin bayar da tallafi.

A auren farko, Wilson da Ann Mutura sun sanya wandon jeans da shat da kuma wasu 'yan ƙarafa da suka yi musaya a matsaya zobe.

Kafofin yaɗa labaran Kenya sun ƙiyasta shagalin aurensu na biyu a kan kuɗi dala dubu 35 a wani waje da ke Nairobi.

Hakkin mallakar hoto AALTONEN JUMBA
Image caption A wannan karo, ma'auratan sun shiga motar ango da amarya kuma sun riƙe furanni

Wakilin BBC ya ruwaito wasu 'yan Kenya na tuhumar masu shirya bikin a kan me ya sa suka kashe irin wannan kuɗi maƙudai wajen biki maimakon tallafa wa ma'auratan.

Sai dai Aaltonen Jumba daga wani kamfanin shirya bikin ya ce ai tuni an tallafa musu.

Ya ce ai tuni sun samu tallafin kuɗi, an ba su gida, an biya musu kuɗin tafiya hutun ma'aurata, an kuma yi musu alƙawarin ba su jari don fara sana'a.

Labarai masu alaka