Guguwar Cyclone Dineo ta kashe mutum 7 a Mozambique

Wasu da ke kokarin tserewa guguwar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana cigabada neman wadanda suka tsira da rayukansu a guguwar

Guguwar Cyclone Dineo ya kashe mutum 7 kuma ya taba mutum 130,000 a yankunan kudancin Mozambique.

Kamfanin dilancin labarai na AFP ya ambato hukumar kula da balo'i na kasa da fadar hakan.

Sun kara da cewa ana cigaba da neman wadanda suka rayu gidajen mutum 20,000 ne suka lalace sakamokon guguwar iska mai karfi da ruwan sama mai karfi.

Guguwar ta fi shafan 'yan garin Inhambane, inda akasarin 'yan yawon bude ido suka fi zuwa wanda ke kudu maso gabashin kasar Mozambique kamar yadda wani dan kungiyar kare hakkin bil adama ya wallafa a shafinshi na tweeter.

Wani hasashen yanayi da BBC ta yi ya yi gargadin cewa ruwan sama mai karfi a kudancin Afirka zai iya jawo ambaliyar ruwa.

Labarai masu alaka