Daruruwan 'yan gudun hijira sun tsallaka zuwa Spaniya

'Yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijira da 'yan sanda da dama sun jikkata a lokacin da wasu daga cikin 'yan gudun hijirar ke kutsawa cikin shingen.

'Yan sanda sun ce kamarar tsaro ya nuna lokacin da 'yan gudun hijirar ke kutsawa cikin daya daga cikin kofofin.

Gwamnatin lardin Ceuta ta ce kusan mutum 500 ne suka tsallaka shingen wanda aka da wayoyi.

Ceuta da Melilla ne kawai garuruwan yankin Spaniya da ke arewacin Afirka wanda ke da ke da iyakar Turai da Afirka.

Wannan dalilin ne yasa ya zama sananniyar hanyar da 'yan gudun hijira wadanda ke sa ran tsallakawa turai ke bi domin fara sabuwar rayuwa.

Wani jami'in gwamnatin Ceuta ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa 'yan gudun hijira 498 sun kutsa kansu cikin yankin Spaniya.

Ya kara da cewa biyu suna asibiti sakamakon jikkata da suka yi a lokacin harin kuma wasu 'yan sanda 11 sun raunana.

Labarai masu alaka