''Yan sanda a DR Congo na nuna karfi a kan masu zanga-zanga'

DR Congo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan adawa na zanga-zanga domin hana shugaba Kaliba saura akan mulki

Wani rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar ta ce jami'an tsaro a Jamhuriyar Demokradiyar Congo na amfani da karfin tuwo a kan masu zanga-zanga a lokacin da suke nuna rashin amincewarsu ta mulkin shugaba Joseph Kabila a karo na uku.

Majalisar ta ce ta na da bayani akan mutuwar akalla mutane 40 da aka kashe a birane daban-daban da ke sassan kasar sakamakon zanga-zangar wadda akayi a tsakanin ranar 15 da 31 ga watan Disambar bara.

Har yanzu gwamnatin kasar bata mayar da martani akan rahoton ba.

Wa'adin shugabancin shugaba Kabila ya zo karshe ne tun a ranar 20 ga watan Disambar da ya gabata, amma kuma sai aka kara zuwa karshen shekarar da muke ciki.

Majalisar Dinkin Duniya ta kulla wata yarjejeniyar da take sa ran za a gudanar da zaben kasar a karshen shekara 2017, inda Mr Kabila ba zai tsaya takara ba.

Labarai masu alaka