Kun san man shafawar da ke kisa?

Phillip Hoe sat in his living room
Image caption Tartsatsin sigarin Philip Hoe ya kama jikinsa wanda aka shafe da maganin fata mai dauke da paraffin

BBC ta gano cewa an alakanta mutuwar gomman mutane a Ingila da amfani da mayukan shafawar da ke dauke da sinadarin paraffin.

Mayukan, wadanda ake amfani da su don magance cutar kyasbi da sauran cututtukan fata, su na iya sanya mutane cikin hadarin da jikinsu zai kama da wuta.

Idan dai har mutane na amfani da mayukan akai-akai, amma ba sa sauya tufafinsu da shimfidar gadonsu, to sinadarin paraffin din na iya ratsawa cikin tufafin, al'amarin da ka iya sanyawa wuta ta tashi.

Hukumar da ke kula da amfani da magunguna ta Ingila, ta gyara fasalin sharuddanta, inda ta ce dole ne a sanya gargadi a dukkan mayukan da ke dauke da sinadarin paraffin.

Duk da cewa an yi gargadin nan fiye da shekara 10 da ta gabata, tashar BBC Radio 5 ta gudanar da bincike, ta kuma cewa mutum 37 ne suka mutu sakamakon amfani da irin wadannan mayuka, tun daga shekarar 2010 zuwa yanzu.

'Shan sigari'

Wata mata mai suna Carol Hoe, ta ce wuta ta kama jikin mijinta Philip a shekarar 2006, sakamakon zubar tartsatsin wutar sigarin da yake zuka a jikinsa, wanda kuma a lokacin yana gadon asibiti ne ana masa maganin wata cuta, kuma an shafe jikinsa da man emollient mai dauke da sinadarin paraffin.

Ta ce, "An yi min waya daga asibitin inda wata ma'aikaciiyar jinya ta ce min lallai na je da gaggawa don Philip ya hadu da wani tsautsayin daban."

"Wuta ta kama jikin Philip. Yana shan taba ne a boye sai tartsatsin wutar ya zuba a jikinsa, sai ya kama da wuta," in ji ta.

una'

Jim kadan da yin haka sai ga Mista Hoe wanda yake karbar maganin wata cutar daban, ya dawo yana jinyar ƙuna a wani asibiti da aka mayar da shi a Sheffield, bai dauki lokaci ba kuma sai ya mutu.

Matar tasa ta ce, "Zuwana wajen ke da wuya, sai ma'aikatan asibitin suka ce min ai ya yi mummunar ƙonewa inda kashi 90 cikin 100 na jikinsa ya ƙone."

"Babu abin da za su iya yi," in ji Misis Hoe.

Wata hukumar bincike kan mutuwar farat daya ce ta jawo hankalin jama'a kan hadarin amfani da irin wadannan mayukan, kuma ita ma hukumar kula da kare marasa lafiya ta bayar da shawara cewa a guji yawan amfani da abubuwan da ke dauke da sinadrin paraffin don suna da matukar hadari, kuma nan da nan za su iya tayar da wuta.

Daga bisani wasu hukumomin lafiya guda biyu sun sake fitar da gargadin, amma an ci gaba da samun mace-macen.

Image caption Christopher Holyoake ya mutu bayan da mayafin gadonsa da ya shafi paraffin residue ya kama da wuta

Wani binciken ya sake gano yadda wani magani na shafawa mai suna E45 ya manne a jikin mayafin shimfidar gadon wani mutum Christopher Holyoake, dan garin Leicester, sakamakon yawan amfani da maganin da yake yi, ba tare ma da izinin likita ba.

A yayin da Mista Holyoake ya kunna sigarinsa, sai wutar ta laso zanin gadon, inda nan da nan wuta ta kama saboda jin kanshi sindarin paraffin da ke jikin mayafin gadon.

Wannan ne ya yi sanadin mutuwar Mista Holyoake mai shekara 63.

Bayan faruwar wannan lamari ne hukumar binciken mutuwar farat daya ta aike da korafinta zuwa ga kamfanin da ke yin wannan magani, inda ta zarge shi da cewa bai rubuta gargadin cewa sinadaria da ke cikin maganin na iya janyo kamawar wuta ba.

Tuni dai kamfanin da ke yin maganin E45 ya amince ya sanya gargadi a abubuwan da yake samarwa, kuma ana sa ran nan da wata guda za a fara ganin hakan.

Haka kuma a shekarar 2015, an kara gano yadda wani dattijo dan shekara 84 John Hills, ya mutu a gidan kula da tsofaffi bayan da wuta ta kama jikinsa, sakamakon lafta wani maganin shafawa mai dauke da sinadarin paraffin, mai suna Cetraben, wanda tuni ya manne a jikin kayansa.

Mista Munro, na hukumar kashe gobara ta London, ya san matsalar sosai, kuma yana kokarin wayar da akai a kanta.

Ya ce, "Na ga irin haka da ya faru sau da dama, kuma tabbas sinadarin maganin ne ke janyowa."

Hukumar kashe gobara ta London ta ce ko da ana yawan wanke kaya ko mayafan shimfidar da ake yawan amfani da su yayin da aka shafa irin wadannan mayuka, to fa hakan ba zai rage hadarin ba, don kuwa shi sinadarin paraffin ya kan dade a jikin abu bai fita ba.

Image caption Fires have been caused when a naked flame has ignited paraffin residue

Labarai masu alaka