Man City ta amince da hukuncin da FA ta yi mata kan rashin da'a

Michael Oliver was surrounded by several Manchester City players after awarding Liverpool a penalty Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan wasan Manchester City sun zagaye Michael Oliver bayan ya bai wa Liverpool bugun fenareti

Man City ta amince da hukuncin da hukumar kwallon kafar Ingila ta yi mata a kan nuna rashin da'ar da 'yan wasanta suka yi domin kin amincewa da bai wa Liverpool bugun fenareti a wasan da suka tashi 1-1 ranar Lahadi.

Hakan ya faru ne a kusan minti 50 da fara wasan, inda a lokacin suke da ci 1-1, yayin da alkalin wasan Michael Oliver ya bai wa Liverpool damar bugun daga kai sai mai tsaron-gida, domin hukunta Gael Clichy saboda tokarin Roberto Firmino.

Wata hukuma mai zaman kanta ce ta saurari karar.

James Milner shi ne wanda ya samu nasarar cin kwallon.

Kwallon da Milner ya ci ya bai wa Liverpool nasara a lokacin, sai dai daga baya Sergio Aguero ya farke cin da akai musu inda daga karshe suka tashi kunnen doki a filin wasan Etihad.

Clichy da David Silva sun yi wa alkalin wasan hayaniya a kan ya bayar da fenareti.

Labarai masu alaka