Za a fara gwada shiga motar da ba matuƙi a Birtaniya

Oxbotica's prototype shuttle Hakkin mallakar hoto Oxbotica

Al'ummar Birtaniya na shirin amfani da mota marar matuƙi a karon farko a ƙasar.

Sama da mutum 100 ne za su ɗana motar a cikin birnin London nan da makonni uku masu zuwa.

Kwamfuta ce za ta sarrafa motar, wacce take tafiyar kilomita 16 a duk sa'a daya.

Haka kuma akwai kwararren mutum da zai kasance a cikin motar, wanda zai iya tsayar da ita idan bukatar hakan ta taso.

Kamfanin Oxbotica, wanda ya ƙera motar, ya ce a yanzu kusan mutum 5,000 ne suka son samun wannan fasaha.

Shugaban Kamfanin Graeme Smith, ya shaida wa BBC cewa, "Mutane ƙalilan ne suka taɓa ganin mota mai sarrrafa kanta, saboda haka wannan dama ce da kowa zai iya ganinta.

"Muna fatan wannan mota za ta samu karbuwa a wajen mutane, domin amfani da ita."

"Kuma za mu sa ido don ganin yadda mutane za su yi tsokaci idan motar ta dauke su daga wannan wuri zuwa wancan."

'Za ku iya shiga?'

Motar tana iya ɗaukar mutum hudu, kuma ba ta da sitiyari da kuma giyar birki.

A lokacin gwajin, za a sanya kamarori biyar da wata na'ura mai haska waje guda uku, wadanda za su taimaka wa motar wajen kewayen da za ta yi na tsawon tafiyar mil biyu, wajen da masu tafiya da kafa da masu keke, ke amfani da shi.

Hakkin mallakar hoto GATEWay
Image caption Titin da motar da za ta dinga bi

Motar na iya hango abu a kan hanya, tun daga nisan mita 100, kuma za ta tsaya idan ta gano akwai wani abu a kan hanyar, kuma ta kan ci burki da gaggawa idan bukatar hakan ta taso.

Dr Smith ya ce, "An yi ta ne don ta zama kariya musamman ma ga wuraren da ake tafiyar kafa."

Jami'an da suka yi wannan motar, sun yi amanna cewa, motar za ta inganata tafiye-tafiye a birnin.

Sun ce fasinjoji za su dinga biyan kudi don shiga motar a shekarar 2019 a wannan yankin, daga nan kuma za a fadada amfani da ita a sauran wurare.

Ministan Masana'antu Nick Hurd, ya ce, "Birtaniya na da tarihin kere-kere ta bangaren abubuwa masu sarrafa kansu, kuma wannan fasaha tana da karfin kare rayuka da kuma sama wa tsofaffin mutane 'yanci, da kuma mutanen da suke da ciwon da ba ya son yawan motsawa."

Sauran gwaje-gwaje

Wannan ba shi ne karon farko da aka gayyaci mutane da su hau gwajin mota marar matuki ba a titunan Birtaniya.

A wani gwaji na baya-bayan nan a Milton Keynes, kamfanin na Oxbotica ya bar 'yan Jarida shiga gwajin wata karamar mota marar matuki, kuma ana fatan za a fara zirga-zirga da ita nan gaba domin inganta tafiye-tafiye.

Haka kuma mutane a wasu wuraren a fadin duniya sun taba ɗana gwajin mota marar matuki .

A watan Janairu kamfanin Las Vegas ya yi gwajin wata motar daukar fasinja marar matuki, wacce za ta yi jigilar fasinjoji a kan titin Fremont Street a birnin da ke da tarihin zirga-zirgar jama'a.

Sannan a watan Agustan 2016 wani kamfanin kasar Singapore mai suna nuTonomy, ya sha alwashin cewa shi ne kamfani na farko da zai kera motoci marasa matuki ga jama'a, ta hanyar amfani da manhajarta ta Taxi.

Ta fara amfani da kananan motoci a yankin da bai wuce nisan mil 2.5 ba a yankin birnin kasar, kuma an takaita zirga-zirgar motocin ne a wadansu wurare .

Labarai masu alaka

Karin bayani