Yadda mutane ke shan gurbataccen ruwa don su rayu

Dubban 'yan gudun hijirar kasar Sudan Ta Kudu ne suka tserewa tashin hankali da yunwa daga kasarsu, zuwa wasu sansanoni da ke arewacin kasar Uganda don tsira da rayukansu. Yanzu haka fiye da mutum 50,000 daga cikinsu na zaune a sansanin Rhino, wani wuri mai cunkoso da kuma dauda kusa da garin Arua.

Rayuwa a sansanin da wahala, amma kowa ya yi amanna cewa rashin ruwa shi ne babban kalubalen da ake fuskanta. Babu rijiyoyin burtsatsai, kuma koguna da ake da su a yankin sun kafe. Ruwan da ake samu ya sauya launi, ba shi da maraba da tabo.

The upper reaches of the White Nile in Uganda Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC

A wani mataki na kawo dauki, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Duniya (Red Cross), ta fara debo ruwa da manyan motocin daukar ruwa daga kogin Nilu, daga nan sai a tsaftace shi ta hanyar bin wasu matakan tsaftace ruwa gabanin a sauke ruwan daga motocin a sanya su a tankuna. Daga nan, sai a biyo ta cikin daji zuwa sansanin, inda a nan ne aka ajiye daruruwan kananan tankunan ruwa, wanda ake cikasu sau biyu ko sau uku a kowace rana.

Ruwan na tahowa daga kogi sannan ya shiga cikin tankuna, ta hanyar yin amfani da famfuna da bututai, inda ake sanya sinadarin Aluminium Sulphate a cikin ruwan don kashe da kwayoyin cuta. Cibiyar ruwan wadda ta fara aiki a farkon watan jiya, tana da ma'aikata 40 daga kasar da kuma kasashen ketare.

Using a system of pipes and pumps, water is drawn from the river into floatation tanks Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC
A member of staff stands on a ladder at the plant Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC

Daya daga cikin ma'aikatan Kamfanin IFRC, Noor Pwani ya ce, "Wannan ce kadai hanyar da za mu magance cututtuka masu yaduwa, babbar damuwarmu shi ne rashin ingantaccen yanayi a cunkoson mazaunin nasu, kuma lokacin damina na zuwa, a lokacin da cututtuka masu yaduwa ta ruwa ke kara bazuwa"

Agaba Derrick ma'aikaci ne mai kula da ruwan kogin, wanda yake kawo sauyi da inganci sa'a bayan sa'a. Ya yi bincike game da adadina sinadarin da ake sanya wa ruwan. Har ila yau, sinadarin Chlorine na kara kashe sauran kwayoyin cutar Bacteria.

24 year old volunteer Agaba Derrick Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC
A lab assistant weighs out a measure of chlorine powder Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC

Lokacin da ruwa yake kwarara daga dayan bangaren, garai yake. Injin na kaiwa ga famfuna adadin da ya kai Lita miliyan daya na tsaftataccen ruwa a kowace rana. Adadin ruwan da mutum daya yake bukata a rana a sansanin shi ne tsakanin Lita 15 zuwa 20 ba, kuma da shi ne mutum zai yi wanki da girki da kuma kashe kishirwa.

Ayarin motocin ruwa guda 30 ne da jirgin fito suke kawo tsaftataccen ruwa mai kyau a raba a sansanin, wanda ake sawu uku a kowace rana. A wasu yankunan an shinfida sabbin kwalta don kaucewa cunkoso ababan hawa.

When the water flows out the other side, it is crystal clear Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC
A fleet of around 30 tankers ferries the clean water to distribution points in the camp Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC
Residents of Rhino camp wait by a water point with the jerry cans, as a tanker offloads its cargo Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC

Monica Achan, wacce ta shafe makonni biyu tana tafiya ta cikin daji don isa kasar Uganda bayan da sojoji suka kashe dan'uwanta, ta samu ta kurbi ruwan kogin Nilu a sansanin.

Sai dai ta ce: "Rayuwa a nan akwai wahala". "Da zarar akwai ruwa, to za mu rayu, rayuwa ba ta yiwuwa sai da shi."

Monica Achan takes a sip of Nile water Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC
A woman draws water from a tap in Rhino camp, where tanks must be refilled up to three times a day Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC
A girl smiles as she fills up her jerrycans with water Hakkin mallakar hoto Tommy Trenchard / IFRC

Wanda ya dauki hotunan ya kuma samo rahoton shi ne Tommy Trenchard.

Labarai masu alaka

Karin bayani