Nigeria: An 'ceto jarirai sama da 200 da aka zubar' a Lagos

Wasu yara suna bacci Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rahotanni sun ce ana yawan zubar da jarirai a Najeriya

Gwamnatin jihar Lagos a Najeriya ta ce ta yi nasarar ceto jarirai 237 da aka zubar a sassa daban-daban na jihar.

Jarirn 106 maza ne, yayin da 131 kuma suka kasance mata, kuma an jefar da su ne a bara.

Jaridar Punch da Guardian, sun rawaito cewa, kwamishinan matasan jihar, Uzamat Akinbile-Yussuf, yana ganin cewa an kara samun yawaitar adadin jariran da aka tsinta a watannin baya-bayan nan.

Yara na baya-bayan nan da aka tsunta su ne guda 53 da aka zubar a kusa da wata bola a jihar.

Wani wakilin BBC a Najeriya ya ce akan jefar da jarirai ne saboda iyayensu talakawa ne ko kuma an haife su ne ba ta hanyar aure ba.

Labarai masu alaka