Nigeria: 'Yan kwadago sun hana gabatar da jawabin minista

Ministan Kwadago na Najeriya, Chris Ngige Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mista Chris Ngige ne ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari a wurin taron

Wasu 'yan kwadago a Najeriya sun hana gabatar da jawabin Minista a Dandalin Eagle Square da ke Abuja, babban birnin kasar, inda aka yi bikin Ranar Ma'aikata ta Duniya.

Sai dai kuma kakakin babbar kungiyar kwadago ta kasa, wato NLC, Kwamared Nuhu Abbayo Toro, ya ce wadanda suka yi hakan sojan haya ne.

Ma'aikatan sun yi ta rera wakokin bijirewa a lokacin da aka ce babbar Sakatariya a Ma'aikatar Kwadago ce za ta yi musu jawabi, a madadin Ministan Kwadago Chris Ngige, kuma yunkurin da aka yi na shawo kansu bai yi nasara ba.

Ministan dai na wakiltar Shugaba Muhammadu Buhari ne a wajen taron.

Daga karshe dai haka Mista Ngige, da ma sauran manyan bakin da suka halarci taron, suka watse ba tare da an gabatar da jawabin ba.

Ma'aikatan da suka bijire sun ce ba su amince wani ya gabatar da jawabi a madadin ministan ba saboda suna bukatar kwakkwaran jawabi game da batun karin albashi ba alkawarin kafa kwamiti ba.

Labarai masu alaka