Kotun kolin India za ta sauya dokar saki uku

Matan Indiya
Image caption Mata a Indiya na yawan kokawa kan yadda maza suka mayar da saki uku ba wani abu ba

Kotun kolin kasar Indiya ta fara sauraron dumbin kararrrakin da suke kalubalantar saki uku nan take.

Kotun ta ce za ta yi bincike ta gani ko yin saki uku a lokaci guda na da nasaba da addinin Musulunci.

Kasar Indiya na daya daga cikin kasashen duniya kalilan da Musulmi zai iya sakin matarsa cikin dakika daya muddun ya furta kalmar 'saki' sau uku.

Sai dai masu fafutuka sun ce yin hakan "nuna wariya ce."

Kungiyoyin Musulmai da dama na yin suka a kan tsoma bakin kotun a al'amuran addini, duk da cewa batun na samun goyon-baya daga gwamnatin kasar ta Firai Minista Narendra Modi.

An samu alkalai biyar daga addinai daban-daban da suka shiga cikin wannan batu mai sarkakiya, daga addinin Hindu, da Sikh, da na Kirsta da Zoarastrian da kuma Musulunci.

Alkalan sun tattara takardun kara da dama na mata Musulmai da kuma kungiyoyin kare hakki domin gudanar da bincike a kan batun.

A shekarar da ta gabata ne, daya daga cikin wadanda suka shigar da kara Shayara Bano, ta yi hira da BBC cewa, inda ta soki lamarin sakin mai cike da ce-ce-ku-ce.

A watan Oktobar shekarar 2015 ne, wata mace mai shekara 35 da yaranta biyu, ta tafi gidan iyayenta da ke Uttarakhand a arewacin kasar don duba lafiyarta, bayan da ta karbi takardar saki daga wurin mijinta.

Ta yi kokarin ta samu mijin nata wanda suka yi shekara 15 tare, wanda yake zaune a birnin Allahabad, sai dai hakan bai yiwu ba.

Ta shaidawa BBC cewa, "Ya kashe wayarsa, kuma ba ni da wata hanyar da zan same shi. Wannan rashin lafiyar na damuna saboda rayuwar yarana na cikin wani hali."

A watan Fabrairun shekarar da ta gabata ne, ta shigar da kara kotun kolin inda take bukatar a haramta saki uku, wanda hakan zai ba wa Musulmai maza damar su rika rike matansu da mutunci".

Duk da an shafe shekaru da dama ana yin saki uku a lokaci guda, matsayar Malamai da dama ita ce cewa ba a samu wani ingantaccen nassi daga Kur'ani ko Shari'a ba.

Malaman addinin Musulunci sun ce, Kur'ani ya yi bayani karara a kan sha'anin saki, kuma za a yi zaman wata uku (idda) wanda hakan zai ba wa ma'aurata damar sasanta tsakaninsu.

Masu fafutuka sun ce, yawancin kasashen Musulmai da suka hada da kasar Pakistan da Bangladesh, sun haramta saki uku a lokaci guda, amma kuma abin na dada bunkasa a Indiya.

A shekarun baya-bayan nan, Musulmai maza da dama na kasar Indiya sun fadawa matansu cewa za su sakesu ta hanyar aika takarda ko wayar tarho, ko ma ta sakon wayar salula.

Abin da mafi yawan Malamai suka yi amanna da shi shi ne cewa, duk da dai Ubangiji ya halatta saki, to ba ya farin ciki da a yi shi ko da sau daya ne, in dai ba kan al'amari mai sauki ba.

Labarai masu alaka