Ko kun san cin naman talo-talo na sa isasshen bacci?

Dr Michael Mosley Hakkin mallakar hoto LION TELEVISION
Image caption Dr Michael Mosley na daya daga cikin wadanda suke fafutikar duk dare don samun isasshen bacci.

Me ya sa Dakta Michael Mosley ya yi bincike a kan abin da ke hana samun isasshen bacci?

Sananniyar al'ada ita ce mu samu baccin dare na sa'a bakwai, yayin da ake son matasa su samu baccin sa'a tara. Amma mafi yawancin mu, ba ma samun ko kusa da hakan.

Wani nazari da wata ƙungiya mai suna "Sleep Council" ta yi, ta gano cewa kashi 22 cikin ɗari na matasa ne ke samun baccin da ake buƙata, na sa'a bakwai zuwa takwas, yayin da kashi 40 cikin ɗari suka ce suna baccin sa'a shida zuwa ƙasa.

Ina ɗaya daga cikin masu fafutikar samun isasshen bacci.

Ba wai ina zuwa yawon dare ba ne, ko kuma don ina da wata matsala da za ta hana ni samun bacci, amma kullum na kan farka da tsakar dare, kuma in yi ta ƙoƙarin komawa bacci amma sai abin ya ci tura.

Domin gano dalili, na rubuta wani littafi mai suna, "The Truth about Sleep" wato sirrin da ke lullube cikin barci, lokacin da na hada kai da wasu manyan ƙwararru, domin gudanar da bincike game da bacci, kuma mun fara gwaje-gwaje a kan mutanen da ke buƙatar bayar da gudunmowa.

Abin da na gano shi ne yayin da wasu mutane ke samun isasshen bacci a ƙasa da sa'a bakwai, mafiya yawanmu ba ma samun hakan.

Baya ga rauni ga ƙwaƙwalwa da gangar jiki da ƙarancin bacci ke haifar mana, wani abu da muke son bayyanawa, shi ne dabarar da ake amfani da ita wajen inganta bacci na taimakawa, sai dai da yawa ana ganin ta kamar ba ta da amfani.

Alal misali cin naman talo-talo na taimakawa wajen samun ingantaccen bacci, saboda yana ɗauke da sinadarin da ake kira tryptophan, wanda zai taimaka maka wajen samun isasshen bacci.

Duk da cewa Talo-talo ba shi da isasshen sinadarin trypophan, amma abin da namansa ke ɗauke da shi ba ya kai wa ga kwakwalwa.

Hanyoyin da za su inganta bacci da muka kawo, waɗanda da ake yi musu kallon mamaki sun haɗa da:

Tashi daga bacci lokaci daya a ko wacce safiya.

Yin sassarfa ko gudu da safe a mafiya yawan ranaku.

Cin kayan marmari na guda biyu sa'a daya kafin kwanciya.

Mayar da hankali kan abu guda daya a lokaci guda, tare da cire ko wanne tunani a rai.

Yin wanka da ruwan dumi sa'a daya ko biyu kafin kwanciya bacci.

Cire na'urorin lantarki daga ɗaki, da kuma kashe talabijin da kwamfyuta da wayoyi da sauran makamantansu, sa'a daya kafin kwanciya.

Ƙauracewa shan giya.

Cin abincin da ke ɗauke da sinadarai da yawa.

Kana samun isasshen bacci?

Ka kwanta a ɗaki marar haske, kuma marar hayaniya, tun da farkon dare, ka ɗora cokali a gefen gadonka.

Ka sanya farantin tasa a kasa, sai ka duba lokaci, sannan ka rufe idanunka.

Idan ka fara bacci, 'yan yatsunka za su turo cokalin ya daki farantin da kara mai karfi, wanda zai tashe ka.

Da zarar hakan ta faru, yi sauri ka duba agogonka, domin ganin lokacin da ka shafe a baccin.

A ganin Farfesa Nathaniel Kleitman, na Jami'ar Chicago:

Idan ka fara bacci mintuna biyar da kwanciyarka, to lallai baccin ya ci karfinka.

Idan kuwa cikin minti 10 da rufe idonka ka yi baccin, to lallai akwai "matsala" kenan.

Idan ka shafe minti 15 a kwance idonka biyu, to za ka samu lafiya.

Hanya mafi sauƙi ita ce, ka saita kararrawar agogo ta minti 15, sai ka rufe idanunka, sai ka gani ko za ka iya yin bacci kafin kararrawar ta buga.

Labarai masu alaka