Sojojin dake bore a Ivory Coast sun ki ajiye makamai

Ivory Coast Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption Sojoji masu yin bore sun rufe birnin Bouake ba shiga ba fita

Babban hafsan sojojin Ivory Coast ya ce rundunar sojin kasar ta kaddamar da wani farmaki na dawo da doka da oda a birni na biyu mafi girma a kasar, Bouake, wanda ya kasance karkashin ikon sojoji masu yin bore.

Jama'a na ci gaba da yin tir da boren da sojojin ke yi, abin da har ya kaiga wasu mutanen yin maci.

Mutane shida ne aka jikkata lokacin da sojojin dake yin boren suka bude wuta kan masu adawa da boren na su.

Sojojin suna yin bore ne saboda rashin biyansu wasu kudaden alawus dinsu, lamarin da yasa suka rufe birnin Bouake, ba shiga ba fita, sannan kuma aka rufe shagunguna.

Sojojin sun ce ba za su ajiye makamansu ba.