"Masu zafin adawa ke yaɗa jita-jitar mutuwar Buhari"

Buhari Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya koma London don sake ganin likita sai dai 'yan Nijeriya sun ƙagara su ji daga gare shi

Wasu masharhanta sun ce jita-jitar mutuwar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da akan yaɗa saboda rashin lafiyarsa, ta samo asali ne tun kafin zaɓen 2015, daga 'yan siyasa masu zafin adawa.

Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya, Dr. Abubakar Kari ya ce masu yin irin wannan fata sun ɗauka suna yin adawa ce, amma dai a gaskiya wannan mummunar adawa ce.

Ya ce a lokacin yaƙin neman zaɓe irin waɗannan 'yan adawa sun yi ta yi wa shugaban fatan mutuwa kafin gudanar da zaɓe.

Ko kuma mutuwar ta riske shi jim kaɗan bayan an yi zaɓe. Sannan kuma a lokacin da ya kamu da rashin lafiya sai suka ci gaba da irin wannan fata, in ji shi.

Ya ce magana ce ta adawa waɗanda suka kitsa wannan jita-jita sun daɗe suna yi.

Hakkin mallakar hoto Presidency

Masanin kimiyyar siyasar ya amsa cewa ba shakka halayyar rashin yi wa 'yan ƙasa bayani lokaci zuwa lokaci game da rashin lafiyar shugaban ya ƙara rura wutar irin waɗannan jita-jita.

Ya ce abin da ya shafi shugaban ƙasa ya shafi zaman lafiyan ƙasa da kwanciyar hankalinta da sha'anin mulki.

A cewarsa kamata ya yi shugaban ko ta shafukan sada zumunta ya riƙa ƙoƙarin bayyana wa 'yan Najeriya halin da yake ciki a London.

Labarai masu alaka