Silva ya koma Man City a kan fam 43m

Silva, Monaco Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Silva ya taka gagarumar rawa wajen nasarar da kulob din Monaco ya samu a Gasar Ligue 1 da kuma matakin gab dana kasar da kulob din ya kai a Gasar Zakarun Turai

Kulob din Manchester City ya saye dan wasan tsakiyar kulob din Monaco Bernardo Silva a kan fam miliyan 43.

Dan wasan mai shekara 22 zai fara taka leda ne a Man City a ranar 1 ga watan Yulin bana. Silva ya ce: "Yanzu zan yi wasa a daya daga cikin manyan kulob din duniya."

Silva ya yi wa Monaco wasa sau 58 a kakar bana - ciki har da wasa biyu da suka buga da Man City a Gasar Zakarun Turai, inda a duka ya ciyowa kulob din kwallaye 11 ya kuma taimaka wajen ciyo kwallo har sau 12.

Hakazalika, ya ce kwadayin yin aiki da Pep Guardiola yana daga cikin abin da ya sanya shi amincewa da tayin da Man City ta yi masa.

"Shakka babu idan mutum ya samu damar yin aiki da Guardiola, ba za ka iya cewa a'a ba," inji dan wasan wanda ya buga wa kasarsa wato Portugal wasa sau 12.

Ya ci gaba da cewa "Idan ba Guardiola ba ne kocin da yafi kwarewa a duniya, to yana daya daga cikin wadanda suka fi kwarewa."

An kammala Gasar Firimiyar bana ne Manchester City tana a mataki na uku, wanda hakan yake nufi cewa ta samu tikitin shiga Gasar Zakarun Turai ta badi.