Mutane miliyan 8 za su iya rasa abinci a Ethiopia

drought Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ethiopia na daga cikin kasashen gabashin Afrika dake fama da fari

Gwamnatin Ethiopia da hukumomin bada agajin jin kai, sun ce kayan abinci da ake ba da tallafin gaggawa ga mutane kusan miliyan takwas da bala'in fari ya shafa, za su kare kare zuwa karshen wanna watan.

Jami'ai sun ce ana bukatar karin kudade, sai dai akwai damuwa kan yadda masu bada tallafin kudaden ke nuna gajiya, inda suke bada taimakon kudaden a wasu yankuna na duniya dake fama da tashe-tashen hankali.

An ta'allaka bala'in farin da aka samu akan ci gaba da rashin saukar ruwan sama.

Wasu sassan gabashin Afirkan ma na fama da bala'in farin.

Ba kamar a Sudan ta Kudu ba, in da rikice-rikice suka haifar da bala'in yunwa, fari a Ethiopia wani bala'i ne da ya fadawa kasar sakamakon rashin ruwan sama.

Wannan dai ba sabuwar matsala ba ce a kasar, kuma yanzu, hukumomin Ethiopian suna kokartawa don rage radadin bala'in, fiye da yadda suke yi a can baya.

Sai dai duk da haka, suna cikin damuwa a bana.

Gwamnatin kasar ba ta da wadataccen abinci, kuma kungiyoyi masu bayar da agajin kudi ba su yi alwashin bada kudade masu yawa ba.