Hukumar Lafiya ta sanar da ɓullar shan inna a DRC

Bayar da maganin cutar shan inna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Allurar Polio

Hukumar lafiya ta Duniya ta gano ɓullar cutar shan inna a wasu sassa biyu na Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

Ta ce akwai matuƙar hatsarin cewa cutar za ta iya bazuwa a wasu wurare cikin kasar .

An samu ɓullar shan innar ce a wasu yankuna da ba su cika samun alluran riga-kafin kamuwa da cutar ba.

Cutar shan inna akasari tana shafar yara ne kuma duk da gangamin kakkaɓe ta a duniya,kuma idan ta kama yaro a karshe zai kasance da musaki.

Cutar ta shan inna na ci gaba da zama alaƙaƙai a Nijeriya da Pakista da kuma Afghanistan kasashen da ake take a dukan tsawon shekara.

Labarai masu alaka