Za a biya kusan N2m ga wanda ya yarda a sa masa cuta

Shin nawa za a biya ka, don a yaɗa maka tarin fuka da gangan saboda gwajin kimiyya? Masu bincike a Jami'ar Southampton ta Ingila na tayin ba da ladan fam 3,526 kusan naira miliyan biyu kan wannan ƙalubale.

Suna son yin wani ingantaccen riga-kafi don kare jarirai da yara 'yan dagwai-dagwai har ma da manyan da ke cikin kasadar kamuwa da wannan cuta.

Don samun wannan dama, sai shekarun mutum sun kai 18-45 kuma sai mai ƙoshin lafiya wanda zai so zama a wani keɓantaccen wuri tsawon kwana 17 yana rera waƙa.

Tofin mai tari

Tarin fuka, wata cuta ce mai saurin yaɗuwa ta hanyar tofar da yawu ko tari daga mutanen da suka kamu.

Ayarin ƙwararru a Southampton na son yaɗa wa mutane masu ƙoshin lafiya ƙwayar wannan cuta (ta hanyar ɗora ƙwayoyin bakteriyar da ake kira pertussis a kan hancinsa) don ganin yadda za su wanye.

Wasu daga cikin 'yan sa-kan za su kamu da rashin lafiya, amma masana kimiyyar sun fi mayar da hankali a kan waɗanda ba a ga kowanne nau'i na alamomin cutar a jikinsu ba, duk da yake, ƙwayar cutar ta shige su ta hanci.

Abin da suke nema a nan shi ne masu ɗauke da cutar a fakaice, da kuma mutanen da tun ainihi suna da kariyar wannan cuta mai yaɗuwa.

Mutanen da ke ɗauke da cutar a fakaice suna yaɗa cutar tarin fuka ga wasu, amma dai su kuma ba ta sa su rashin lafiya ba.

Ga alama suna da isasshen garkuwar cutar tarin, duk da yake ba a yi musu riga-kafi ba.

Akwai mutane ƙalilan, waɗanda su kwata-kwata ba sa kamuwa.

Hakkin mallakar hoto Prof Rob ReadImage copyrightUNIVERSITY HOSPITAL SO
Image caption Farfesa Robert Read ya ce 'yan sa-kan sun cancanci samu lada saboda lokacin da za su bayar

Fahimtar hakan za ta taimaka wajen ƙirƙiro wani riga-kafi mai matuƙar inganci.

Jagoran masu binciken, Farfesa Robert Read na cewa: "Muna son sanin wacce irin baiwa ce da su, kuma me ya sa ba za mu iya harbarsu da cutar ba, har su dinga yaɗa ta a fakaice."

Yaɗa cutar da gangan

Gwajin ta hanyar amfani da bil'adama na Farfesa Read, ɓangaren wani binciken haɗin gwiwa ne na fam miliyan 24 da ke samun tallafin Gidauniyar Bill da Melinda Gates, gami da wasu kamfanonin haɗa magunguna, don ƙirƙiro wani sabon riga-kafi mai inganci.

Farfesan yana buƙatar mutum 35 da za su taimaka masa da ayarin ƙwararrun da ke tare shi a matakin farko na wannan aiki.

Da zarar an harba musu ƙwayar cutar da gangan, 'yan sa-kan waɗanda za su karɓi wannan lada, za su zauna a wani keɓentaccen wuri a cibiyar binciken tsawon kwana 17.

Za a sanya su a wani ɗaki, inda za su iya zuwa banɗaki, su yi wanka a shaya har ma a ba su kayan shaƙatawa.

Za a kawo musu abinci da abin sha da 'yan toye-toye da lashe-lashe, amma za su riƙa sanya wani abin rufe fuska idan sun yi wani baƙo ko kuma a lokacin da za su yi hulɗa da wani ma'aikaci don ganin ba su yaɗa wa wani ba.

Za a riƙa tsane danshin hanci da na maƙogwaron mutanen da za su shiga gwaji a tsawon lokacin wannan bincike, za kuma a buƙaci ɗaukar majina inda za a ce su fyato hanci, kuma za a sanya wata 'yar takarda a kan hancin nasu tsawon minti biyar a wani lokaci.

Hakkin mallakar hoto UNIVERSITY HOSPITAL SOUTHAMPTON NHS FOUNDATION TRU
Image caption A irin wannan gilashin za a sa 'yan sa-kan a lokacin bincike

Za kuma a ce wa masu sa-kan su zauna a cikin wani akwaitin gilas kuma su yi magana, da tari har ma su rera waƙa ta yadda yawunsu zai riƙa fallatsa cikin iska don masu binciken su ɗauki samfuri.

Za kuma a yi musu jarrabawa kan halayya a iya zaman da za su yi, don auna lafiyar ƙwaƙwalensu.

Kafin a bar su su koma cikin mutane, za a ba su magungunan kashe ƙwayoyin cuta don share ƙwayoyin baktreriyar da aka harba musu.

Labarai masu alaka