An kashe 'yan Boko Haram '13' a ƙauyen Gumsuri

Wani soja rike da bindiga Hakkin mallakar hoto Getty Images

Rahotanni daga jihar Borno sun ce akalla mayakan Boko Haram 13 ne suka mutu bayan wani hari da suka kai ƙauyen Gumsuri da ke jihar.

Wani ganau da bai amince a bayyana sunansa ba ya shaida wa BBC cewa maharan sun mutu ne a cikin wata bata-kashi da mutanen garin da kuma sojoji da mayakan sa-kai da suka kawo dauki ga kauyen na Gumsuri da yammacin ranar Assabar.

"Kamar karfe 4:30 na yamma ne suka shiga. An yi bata-kashi da su da sojoji da suka kawo mana dauki. Sun yi mana taimako da su da yaran gari. An kashe musu guda 13 kuma an karbo bindigogi 13," in ji shi.

Sai dai ya ce biyu daga cikin mutanen garin su ma sun rasa rayukansu.

A cewarsa sai dai sun kokkone wasu wurare a garin kuma sun yi awon-gaba da wasu kayayyaki, kodayake daga baya kwato su.

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar wa BBC aukuwar al'amarin.

Mai magana da yawun sojin kasar Brigediya Janar Usman Kukasheka ya ce za su iya tabbatar da mutuwar 'yan Boko Haram 10 ne kawai saboda gawawwakin mutum 10 kawai suka samu.

Har ila yau ya ce babu wani soja ko farar hula da ya mutu, ko ya jikkata.

A makon da ya gabata, jami'in hulda da rundunar 'yan sanda a jihar ya tabbatar da cewa 'yan Boko Haram na kai farmaki yankin da kauyen yake, domin neman abinci. Amma ya ce jami'an tsaro na fatattakar su.

Labarai masu alaka