Kun san al'ummar da ke mu'amala da birrai a kasar Ghana?

Birai
Image caption Al'ummar dake mu'amala da birai a Ghana

A kasar Ghana da alamu wasu namun daji na fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa, saboda aikace -aikacen dan Adam.

Daya daga cikin abubuwan da ke haifar da hakan akwai irin su sare gandun daji, da farauta da kuma hakar ma'adanai da ake yawan yi ba bisa ka'ida ba.

Wadanda wannan lamari ya fi shafa dai sune mazauna garin Buabeng Fiema da ke jihar Brong Ahafo.

Garin dai na kusa ne da wani daji da ke da tarin birrai.

A ko wace rana dai wadannan birrai na shiga gidajen mutane inda suka zama kamar danginsu.

Image caption Al'ummar garin Buebeng Fiema na daukar birai a matsayin wasu daga cikin danginsu

Akwai garuruwa da dama dai da ake gudanar da mu'amala tsakanin mazauna wuraren da kuma namun dajin da ke kewaye da su musamman birrai.

Sai dai garin na Buebeng Fiema shi ya fi fice inda mazauna garin suka yi imanin cewa ma'amala da birran abu ne da suka gada tun kaka da kakanni.

Hakan ya sa har abinci su kan bai wa birran idan suka kai musu ziyara gida kamar yadda suke yi kullum.

Hasalima har makabarta ta kan su suka ware musu, kana farauta da cin naman birran ya haramta a gare su.

Idan wani birin ya mutu mazauna garin ne ke masa jana'iza ta musamman tare da zaman makoki kamar dan uwansu mutum.

A yanzu haka dai garin ya zama wurin ziyara ga masu yawon bude ido daga kasashen duniya daban-daban.

A baya-bayan nan masana kimiyya da halayyar dan adam sun yi gargadin cewa idan ba a dauki matakai ba kan lokaci, to za a wayi gari wadannan birai da wasu namun dajin za su bace saboda aikace-aikacen dan adam.

Labarai masu alaka