Kenya: An yanke wa mazan da suka yi wa wata zigidir hukuncin kisa

Kenya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daruruwan mata sun yi maci a Nairobi karkashin taken #MyDressMyChoice wato tufafina

Wata kotun Majistare a Nairobi babban birnin Kenya ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa saboda yi wa wata mace zigidir da yi mata fashi da kuma far mata a cikin motar bas, a wani al'amari da aka nada kuma aka yada sosai ta shafukan sada zumunta shekara uku da ta wuce.

An yanke musu hukuncin kisa ne bayan an same su da laifin fashi da makami.

Sai kuma hukuncin daurin shekara 25 saboda yi wa matar Jilo Kadida, zigidir kamar yadda wani mai aikawa jaridar Star ta Kenya labarai ya shaida wa BBC

Ta ce sai dai an jingine hukuncin daurin tun da an yi musu hukuncin kisa.

Mutanen su uku akwai direban mota Nicholas Mwangi da karen mota, Meshack Mwangi da kuma Edward Ndung'u.

Babban majistaren Nairobi Francis Andayi ya ce harin "rashin kan gado ne da rashin mutunci ne ganin yadda suke nishadi da sowa a lokacin da suke tube matar, kamar yadda jaridar Daily Nation ta ruwaito.

Matar da abin ya faru a kanta ta fada wa kotu cewa mutum bakwai ne a motar bas din ne suka so yi mata fyade a lokacin farmakin, ba don ta yi karyar cewa tana da cuta mai karya garkuwar jiki.

Ta ce bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta ya dauki tsawon dakika 59 ne kawai, amma tasirinsa zai shafe tsawon lokaci, a cewar Daily Nation.

Bidiyon harin ya haddasa zanga-zanga, inda daruruwan mata suka yi maci a Nairobi karkashin taken #MyDressMyChoice wato tufafina, sai yadda na ga damar sawa, bayan rahotanni sun ce maza sun far mata ne bisa zargin yin "shigar da ba ta dace ba" da gajeren siket.

Labarai masu alaka