An kashe 'yan Shi'a ashirin a Afghanistan

Ana yi wa birnin Herat, wanda ke kusa da Iran, kallo a matsayin wurin da aka fi zaman lafiya a Afghanistan. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yi wa birnin Herat kallo a matsayin wurin da aka fi zaman lafiya a Afghanistan.

Wani bam da ya fashe a wani masallaci da ke birnin Herat da ke Afghanistan ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 20 sannan ya jikkata mutane da dama.

Bam din, wanda ya fashe a masallacin Jawadia, ya tashi ne lokacin da ake sallar Magriba.

Wani likita ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa an kai gawar mutanen asibiti.

Jami'ai sun ce daya daga cikin maharan dan kunar bakin wake ne, na biyun kuma na dauke da bindiga.

Dukkansu sun mutu, a cewar wani kakakin rundunar 'yan sanda, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Reuters ya ruwaito cewa an yi ta harba gurneti-gurneti a lokacin da aka kai hari.

An ba da rahoton jikkatar mutum 30, kuma ana sa ran wadanda suka mutu za su karu.

Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, wanda ya auku a yankin da mabiya Shi'a suka fi yawa.

Ana yi wa birnin Herat, wanda ke kusa da Iran, kallo a matsayin wurin da aka fi zaman lafiya a Afghanistan.

Labarai masu alaka