Za mu sa kafar wando daya da masu karya doka - Kwastam

Hameed Ali
Image caption Kanal Ali ya ce nan ba da dadewa ba za a daina shigo da shinkafa daga kan tudu da kuma ta ruwa

Konturola Janar na hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya, Kwastam, Kanal Hamid Ali, ya ce hukumar za ta saka kafar wando daya da duk mutanen da ke cewa sun fi karfin doka ta yi aiki a kansu.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne bayan kama buhunan shinkafa da manyan motoci na alfarma da aka shigo da su daga kasashen ketare ta haramtacciyar hanya.

Kanal Ali ya kara da cewa, nan ba da dadewa ba za a daina shigo da shinkafa daga kan tudu da kuma ta ruwa.

A ranar Talata ne hukumar Kwastam ta shaida wa manema labarai cewa ta kama wasu manyan motci na alfarma 37 da buhun shinkafa 12,000 da kuma buhun tabar wiwi sama da buhu 40.

Ga dai karin bayanin da Kanal Ali ya yi wa wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da Hamid Ali kan hukunta masu laifi

Labarai masu alaka