Burkina Faso: An kashe mutum 17 a Ouagadougou

Masu kai dauki tare da wadanda suka jikkata Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane 17 ne suka mutu a harin na Aziz Restaurant

Rahotanni sun ce da misalin karfe 12:00 daren Lahadi aka fara ji tashin harbin bindiga a wani gidan cin abincin Turkawa da ake kira da Aziz Istanbul Restaurant, a birnin na Oaugadougou.

Gwamnatin kasar ta ce kawo yanzu mutum 17 ne suka mutu a harin sannan 8 sun samu raunuka.

Tuni kuma jami'an tsaro suka killace yankin da al'amarin ya auku.

Wurin dai bai shi da tazara sosai da wani otal da kuma wani wurin shan shayi da aka taba kai irin wannan hari a watan Janairun 2016 wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30.

Wata kungiya mai biyayya ga kungiyar mayakan Al'Qaeda mai suna Ansarul Islam ce ta dauki alhakin kai harin na bara.

To sai dai har kawo yanzu ba a samu wata kungiya ko mutum ba da ya irin wannan ikrarin ba dangane da harin na daren na Lahadi.

Sai dai kuma tuni wasu suka fara nuna wa kungiyar ta Ansarul Islam yatsa.

Gwamnatin kasar ta Burkina Faso ta ayyana kungiyar Ansarul Islam wadda, Malam Ibrahim Dicko, wani mai tsattsauran ra'ayin addini da ke jagoranta, a arewacin kasar.

A baya-bayan nan ne dai za a iya cewa kasar ta Burkina Faso ta bi sahun sauran kasashen Afirka ta Yamma da ke fama da hare-haren ta'addanci.