Everton za ta dauki Sigurdsson

Everton Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gylfi Sigurdsson ya yi wa Tottenham da Reading da Shrewsbury ada kuma Crewe

Everton na daf da sanar da daukar dan kwallon Swansea City, Gyfli Sigurdsson kan kudin da ake cewa zai kai fam miliyan 45.

Kocin Everton, Ronald Koeman ya fada a taron da ya yi da 'yan jarida a ranar Laraba cewar likitocin kungiyar sun kammala duba lafiyar dan wasan mai shekara 27.

Dan wasan na tawagar Iceland ya ci kwallo tara ya kuma taimaka aka ci 13 a bara, inda ya bai wa Swansea damar ci gaba da zama a gasar Premier.

Sigurdsson zai zama dan wasa na biyu mafi tsada da Everton ta saya, bayan Romelu Lukaku da ta dauka kan fam miliyan 31.8 daga Chelsea a 2014.