Ana yada jawabin Shugaba Buhari na karya

Shugaba Muhammadu Buhari
Image caption Kwanaki sama da 100 shugaban ya kwashe a birnin Landan yana jinya

Gabannin yada jawabin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan kasar, wasu kafafen sada zumunta sun yada wani jawabi na karya da sunan shugaban ne ya yi wa 'yan Najeriyar.

A jawabin an fara ne da yi wa 'yan kasar godiya, bisa yadda suka yi ta addu'o'in samun lafiya ga shugaban har zuwa dawowarsa a ranar Asabar din karshen mako.

Jawabin ya ci gaba da cewa Shugaba Buhari ya yi godiya ta musamman ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, saboda jajircewa da daukar nauyin kula da kasar da muhimman abubuwan da suka dinga tasowa a lokacin yana birnin London.

Ya godewa 'yan majalisun kasar, da ministoci da bangaren shari'a da ma'aikatu, da jami'an tsaro daga soja har 'yan sanda, da ma'aikatan gwamnati da daukacin 'yan Najeriya baki daya da suka ci gaba da bai wa gwamnati goyon baya duk kuwa da cewa ba ya kasar.

Jawabin ya kara da cewa ko wanne dan adam zai iya fuskantar rashin lafiya, sai dai ba ya fatan ko makiyinsa ya samu kansa cikin halin jinyar da ya samu kansa a ciki.

"Ga wadanda suke tsoro ko tababar rashin lafiya ba za ta bar shi ya ci gaba da jan ragamar kasar nan ba,yana son tabbatar musu da cewa ba u abin da zai faru zai iya ci gaba da jajircewa don cika alkawuran da ya daukar wa 'yan kasa gabannin zabensa.

"Ina da 'yancin zuwa asibiti a ko'ina don neman lafiyata, wanda kuma iyalina da 'yan uwa da abokan arziki ne suke daukar nauyin duk abin da za a kashe a asibiti.

"A matsayinmu na shugabanni yana da kyau mu yi abin da za a yi koyi damu, a lokacin yakin neman zabe na yi alkawarin kawo karshen zuwa kasashen waje don neman lafiya.

"Shekara biyu da hawanmu kan mulki hakan ba ta samu ba, zama na a Birtaniya na sama da kwana 100 shaida ne kan haka, hakika mun magaza kamar yadda muka gaza cika dumbin alkawuran da muka daukarwa 'yan Najeriya.

"Na yi alkawarin cikin sauran lokacin da ya rage min a matsayin shugaban Najeriya, ba zan kara bari wani shugaba ya tafi kasar wajen don neman magani ba.

"Cikin shekarun da muka kwashe a kan mulki, mun bai wa matasa dama da ake tafiya da su a mulki, dubban matasa sun ci gajiyar shirinmu na N-Power, sannan mun ciyar da dalibai yara na jihohi 13 na kasar nan abincin rana kyauta don saukakawa iyaye halin da kasarmu ke ciki na matsin tattalin arziki.

Haka kuma a jihohi tara na Najeriya, fiye da mutane 26,000 na karbar tallafin Naira 5000 a kowanne wata, mun daidaita farashin Naira da daidato a tattalin arzikinmu. Sannan mun tashi tsaye a yaki da cin hanci da rashawa duk da cewa har yanzu akwai jan aiki a gabanmu amma dai mun yi kokari a wannan fannin.

Duk da cewa har yau ba a gani a kas na sauye-sauyen da muka yi alkawari ba, amma da babu gwara ba dadi. A yakin da muke yi da cin hanci da rashawa yawancin mutanenmu da abin ya shafa sun kasa fahimtar duk inda ake son gyara sai an bata.

Ina farin cikin sanar da ku, na dawo bakin aiki cike da burikan da za su kawo ci gaban kasarmu, da habaka tattalin arzikinmu a dan takaitaccen lokacin da ya rage min amatsayin shugabanku.

Zan cika alkawarin samar da kasa mai dorewar tattalin arziki da hadin kai.

Allah ya albarkaci kasar mu, ameen.

Labarai masu alaka