Argentina: An harbe tattabara mai kai miyagun kwayoyi kurkuku

An samu miyagun kwayoyi a jikin tattabarar Hakkin mallakar hoto AL- RAI
Image caption An samu miyagun kwayoyi a jikin tattabarar

Hukumomin gidan yari a Argentina, sun ce 'yan sanda sun harbe wata tattabara, wacce aka aika ta kai wa wasu fursunoni miyagun kwayoyi a wani kurkuku.

Jami'ai sun hangi tattabarar ta sauka a harabar gidan yarin da ke birnin Santa Rosa.

'Yan sandan, sun samu wata karamar jaka a jikin tattabarar, wacce ke dauke da kwayoyi, da wiwi da kuma na'urar adana bayanai wato memory card.

Hukumomin dai na sane da cewa, tsawon wasu shekaru yanzu, ana amfani da tattabara wajen fasakwaurin kananan kayayyaki.

A farkon wannan shekarar, an kama wata tattabara dauke da jaka wacce ke kunshe da miyagun kwayoyi dari da saba'in da takwas a Kuwait, kusa da iyakar Iraki.

Labarai masu alaka