Ambaliya: Venezuela za ta taimaka wa Amurka

Aikin ceto da jirgi mai saukar ungulu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Venezuela ta ce za ta manta da bambancin siyasar da ke tsakaninta da Amurka, domin taimaka wa jama'a

Venezuela ta ce za ta bayar da agajin dala miliyan biyar domin taimaka wa wadanda bala'in guguwa da ambaliyar nan Hurricane Harvey ya fada wa, domin sake gina gidajensu a Texas.

Ministan harkokin waje na Venezuelan Jorge Arreazza, ya ce za a samo kudin ne daga kason cinikin da ake yi a gidajen sayar da mai mallakar kamfanin Amurkar Citgo, wanda tare da kamfanin mai na Venezuelan suka mallaki harkokin man kasar.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Donald Trump ta hari Shugaba Nicolas Maduro da takunkumi

Mr Arreazza ya ce, Venezuela ta zabi kawar da kanta daga bambancin siyasar da ke tsakaninta da gwamnatin Shugaba Trump domin tausaya wa mutanen.

Amurka ta hari kamfanin Citgo da takunkumin da ta dauka a kan Venezuela a watan da ya wuce, a kan zargin cewa Shugaba Nicolas Maduro ya keta 'yancin dan adam da kuma dimokuradiyya a kasar.