Yakin Duniya na 2: Poland za ta nemi diyya daga Jamus

Mr Witold Waszczykowski, Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Minista Witold Waszczykowski ya ce yana shirya yadda kasarsa za ta tunkari Jamus a kan diyyar da za su nema

Ministan harkokin wajen Poland Witold Waszczykowski, ya ce gwamnatin kasarsa na son yin tattaunawa ta musamman da Jamus kan neman biyansu diyya ta barnar da Jamusawa suka yi musu a lokacin yakin duniya na biyu.

Mista Waszczykowski ya ce mamayewar da sojojin Nazi, na Hitler, suka yi wa Poland a shekarar 1939, da kuma bannar da ta biyo baya ta lokacin yaki, har yanzu sun hana wanzuwar alakar kasashen biyu yadda ya kamata.

Ministan ya ce har yanzu Poland tana shirya yadda za ta bullo wa lamarin a hukumance, amma dai gwamnatin ta yi kiyasin cewa za ta nemi Jamus din ta biya ta kusan dala miliyan dubu sau dubu daya, wato tiriliyan daya.

A lokacin da Ministan yake furta kalaman, ya ce kasarsa ba ta samu diyyar da ya kamata a ce an biya ta ba, ta irin dimbin bannar da aka yi mata da wahalar da aka jefa ta, a lokacin yakin, wanda Jamusawan karkashin gwamnatin Nazi suka yi.

Idan aka yi la'akari da girman kasar ta Poland to za a ce, babu wata kasa da ta fi ta asara ta rai da kuma dukiya a yakin duniyar na biyu, domin an hallaka 'yan kasar sama da miliyan biyar, kuma miliyan uku daga cikinsu Yahudawa ne.

Image caption Bannar da aka yi a Poland lokacin yakin duniya na biyu

Sojojin Nazi, na Hitler sun yi kaca-kaca da babban birnin kasar Warsaw, daga titi zuwa titi a lokacin yakin.

Mista Waszczykowski ya ce yana kokarin shirya matsayin da gwamnatinsa za ta gabatar na neman diyyar wannan barna da Jamusawan suka yi musu a wancan lokaci, lamarin da har yanzu ke tsakanin alakar kasashen biyu, na Polanda da Jamus.

A shekarar 1953 gwamnatin gurguzu ta Poland ta ajiye duk wata bukata ta neman diyya daga gwamnatin Jamus ta Gabas.

To amma kuma gwamnatin kasar ta yanzu ta ce wancan matsayi ba shi da tushe, saboda gwamnatin lokacin ta 'yan amshin shatan Tarayyar Soviet ne.