Da gaske Nigeria ta fita daga matsin tattalin arziki?

Sai dai duk da haka 'yan Najeriya sun ce kayana masafuri basu sakko ba
Image caption Sai dai duk da haka 'yan Najeriya sun ce kayana masafuri basu sakko ba

Wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics, NBS, ta fitar ya nuna cewa kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta fada.

Rahoton ya ce tattalin arzikin ya bunkasa da kashi 0.55 cikin 100 a rubu'i na biyu na shekarar 2017 idan aka kwatanta da rubu'i na biyu na shekarar 2016.

Hakan yana nufin cewa girman wannan bunkasa da aka samu ya haura wanda aka samu a rubu'i na biyu na shekarar 2016 da kashi 2.04 cikin 100.

Tattalin arzikin kasar ya samu wannan tagomashi ne bayan da ya kwashe rubu'i biyar yana ci gaba da tsukewa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rashin ciniki na addabar 'yan kasuwa da dama saboda faduwar darajar Naira

A lokacin da tattalin arzikin ya bunkasa, ana fitar da gangar danyen mai 1.84m a kowacce rana, in ji NBS.

Ta kara da cewa, baya ga man fetur, harkar noma da inshora da gas da lantarki na cikin abubuwan da suka taimaka wajen bunaksar tattalin arzikin.

Labarai masu alaka