'Ministocin Buhari da dama na da 'yan takararsu a 2019'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Ministoci na da 'yan takararsu a 2019'

Kuna iya sauraron hirar ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke jikin hoton ministar a sama.

Ministoci da dama a cikin gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari suna da 'yan takararsu daban da shi a shekarar 2019, in ji ministar harkokin mata Aisha Jummai Alhassan.

Ta shaida wa BBC cewa, "A wannan majalisar ministoci akwai 'yan PDP, ba 'yan APC kadai ba; sannan a cikinmu 'yan APC akwai wadanda suke goyon bayan masu neman takarar shugaban kasa a 2019 daban-daban".

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aisha Alhassan ta ce Atiku Abubakar ne gwaninta

Minista Jummai ta ce akwai ministocin da ke cikin gwamnatin Buhari wadanda ba sa so a alakanta su da jam'iyyar APC mai mulki "domin kuwa su 'yan PDP ne".

Ta kara da cewa a shekarar 2019 tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar za ta mara wa baya "saboda shi ne uban gidan siyasata kuma Baba Buhari ya ce ba zai sake yin takara ba".

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aisha ta ce Shugaba Buhari ba zai tsaya takara ba a 2019

Ta yi wannan kalami ne a daidai lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasar ya ya caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan al'amura da dama da suka hada da korafin da ya yi na watsi da shi da aka yi a tafiyar da harkokin gwamnatin.

A wata hira da gidan rediyon VOA Hausa, Alhaji Atiku ya ce jam'iyyar APC ba ta yi da shi duk kuwa da irin taimakon da ya yi wajen kafuwarta da gwagwarmayar da ya yi wajen ganin an kayar da jam'iyyar adawa ta PDP.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce: "Ina cikin jam'iyyar APC da ni aka yi yawo aka yi kamfe amma tun da aka kafata ba a sake bi ta kaina ba an mayar da ni saniyar-ware, ba ni da wata dangantaka da gwamatin, ba a taba tuntubata ko da sau daya don jin ta bakina a ko wacce harka ba, ni ma shi ya sa na janye jikina."

Labarai masu alaka