Hotunan abin da ya faru a Afirka a makon jiya

Jerin hotuna masu kayatarwa na 'yan Afirka daga sassa daban-daban na Afirka a makon nan.

A woman sings during the concert of Malian musician Sidiki Diabate at Modibo Keita Stadium in Bamako on September 3, 2017. Diabate is one of the most popular Afro Trap singers in Mali and Africa. He also plays the kora and contributed to the album Lamomali with Matthieu Chedid and his father renowned kora player Toumani Diabate. Hakkin mallakar hoto AFP

Masoya mawakin 'Rap' dan kasar Mali, Sidiki Diabate na rera waka tare da shi a lokacin da yake wani wasa a filin wasa na Modivo Keita a ranar Lahadi. Diabate dan shahararren mawakin Kora ne, Toumani Dibate, kuma shi ma kwararren mawakin Koran ne na kashin kansa, kumayana daya daga cikin shahararrun mawakan nau'in wakokin 'afro trap' - wanda ya ke hada tsarin waken afirka da na kudancin Amurka.

Mrs. Gabon Gwen Madiba reacts after her crown fell on the floor and is re- placed by television host and personality Arthur Evans (R) during the Mrs. Universe beauty pageant on September 02, 2017, at the International Convention Centre in Durban. Mrs. Universe must age 25 to 45, have a family, her own career, and be involved with a significant cause in favour of other people. Hakkin mallakar hoto AFP

Sabuwar zababbiyar mace mafi kyau a Gabon, Gwen Madiba ke dariya a lokacin da mai gabatarwa a bikin ke mayar mata da alamar sarautar da aka nada ta bayan da ta fadi a kasa. Ita ce tayi ta biyu a gasar Miss Universe da aka yi a birnin Durban na Afirka ta Kudu, gasar da kowace mace mai shekaru 25 zuwa 45 wacce kuma ke da iyali, da aikin yi kuma tana ayyukan jin kai.

A palace guard stands in front of the Emir"s palace before the start of the Durbar festival, on the second day of Eid al-Adha celebration, in Nigeria"s northern city of Kano September 2, 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters

A ranar ce kuma wani dogari ya tsaya a gaban fadar Sarkin Kano gabanin bikin Durbar da aka yi a lokacin bukukuwan Sallah babba a arewacin Najeriya.

Pope Tawardros II delivers morning Mass at St Mary ^ St Mina Cathedral on September 1, 2017 in Sydney, Australia. Pope Tawardros II is visiting Sydney, Canberra and Melbourne during his 10 day pastoral visit. Australia is home to the third largest Coptic community outside Egypt. Copts began arriving in Australia in 1969 and there are now over 100,000 who call Australia home. Sydney has some 70,000, and its Diocese now comprises 41 churches, 70 priests, three schools, two monasteries and two Theological Colleges. Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Jumma'ah babban shugaban cocin Kibdawa, Tawardros na biyu, ya gabatar da jawabinsa na addini ga mabiya a cocin St Mina dake birnin Sydney, na kasar Australia. Kasar ta Ostreliya ce ta uku wajen yawan mabiya darikar ta Kibdawa a wajen kasar Masar.

People manually remove water hyacinth weed from Lake Tana in Bahir Dar, Amhara region in northern Ethiopia, September 1, 2017. Picture taken September 1, 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters

A ranar Jumma'ar ce kuma wasu matasa ke aikin cire tsiron 'hyacinth' daga cikin tafkin Tana dake arewacin Habasha. Wannan tsiron na barazana ga yawan kifin da masunta ke iya kamawa a gabashin Afirka.

A supporter of The National Super Alliance (NASA) opposition coalition and its presidential candidate Raila Odinga sits on top of a street sign post that has been relabeled "Judge Maraga Street", referring to Chief Justice David Maraga, and "Orengo Street", referring to NASA"s lawyer James Orengo, in front of the Supreme Court in central Nairobi, Kenya, 01 September 2017. Kenya"s Supreme Court on 01 September overturned the re-election of President Uhuru Kenyatta and ordered a re-run of the election within 60 days, citing irregularities. Ecstatic opposition supporters marched through the city to celebrate "historic" court decision. Hakkin mallakar hoto EPA

A ranar ta Jumma'a ne kuma wani dan kasar Kenya ya dare saman alamar dake nuna sunan layuka dake kusa da kotun kolin kasar inda alkalin-alkalan kasar David maraga ya soke zaben shugaban kasar da aka yi a watan Agusta. Wasu 'yan kasar sun sauya sunayen titunana birnin domin nuna farin cikinsu da wannan hukuncin na kotun kolin, da kuma lauyan da ya shigar da karar James Orengo,

Egyptian fans cheer for their national team during the FIFA World Cup 2018 qualification football match between Egypt and Uganda at the Borg al-Arab Stadium near Alexandria on September 5, 2017. Hakkin mallakar hoto AFP

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Masar ke taya kungiyar tasu a lokacin wasan samun cancantar zuwa gasar kofin Duniya inda ta ci Yuganda 1-0 ranar Talata. Dan wasan tsakiya na Masar, Sam Morsy yace kungiyar tasu mai suna Pharaohs ta 'kara matsawa kusa' da zuwa gasar da ya gagare su tun 1990.

King Willem-Alexander of the Netherlands (L) receives the letter of credence from the ambassador of Chad, Ammo Aziza Baroud, at Palace Noordeinde in The Hague, the Netherlands, on September 6, 2017. Hakkin mallakar hoto AFP

Sabuwar jakadiyar kasar Chadi a Holland, Ammo Aziza Baroud ke mika takardar kama aiki ga sarki Willem-Alexander a Fadar Noordeinde dake birnin The Hague ranar Laraba.

A security forces member stands in guard during the release of Anglophone activists at the prison of Yaounde,Cameroon, September 1, 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani daga cikin jandarmomin kasar Kamaru ke gadin wani gidan yari a lokacin da aka saki wasu 'yan tawaye daga gidan yarin Yaounde babban birnin Kamaru a ranar Jumma'a. Shugaba Paul Biya ya sanya hannu a kan wata doka domin sakin wasu daga cikin fursunonin da ke tsare a gidan yarin. Ba san halin da sauran 'yan uwansu dake tsare ke ciki ba.

A man cleans the tomb of Mobutu Sese Seko, the late dictator of the self-styled "King of Zaire", which was later renamed the Democratic Republic of Congo after his overthrow, in the European cemetery in Rabat on September 3, 2017, four days before the 20th anniversary of his death. Mobutu died on September 7, 1997 at the Mohamed V military hospital in Rabat after a long battle with prostate cancer. Twenty years on from his death in exile in Morocco, the simple initials MSS on a family grave mark the resting place of Mobutu Sese Seko, the self-styled "King of Zaire". Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Lahadi kuma, wani mutum ke goge alamar sunan tsohon shugaban Zaire, Mobutu Sese Seko a birnin Rabat na Morocco. Tsohon shugaban wanda mai mulkin kama karya ne a lokacin rayuwarsa, ya taba ayyana kansa a matsayin "Sarkin Zaire", amam yanzu kasar ta koma Democratic Republic of Congo, kuma cutar kansa ce tayi sanadiyar mutuwarsa a wani asibitin Rabat shekara 20 da suka gabata. An yi wani taron tunawa da shi a birnin a ranar Alhamis.

Hakkin mallakan hotunan: AFP, EPA, Getty Images da Reuters

Labarai masu alaka