Girgizar kasa mafi muni a shekara 100 ta afka wa Mexico

Damage in the Mexican city of Oaxaca, about 300km from the epicentre Hakkin mallakar hoto EPA

Wata girgizar kasa, wacce shugaban Mexico ya bayyana ta da cewa wacce ta fi ko wacce muni cikin shekara 100 da suka gabata ta afka wa yankin gabar teku na kudancin Mexico, kuma ta yi sandiyyar mutuwar mutum 16.

Girgizar kasar wacce shugaban kasar Enrique Peña Nieto ya ce ta kai karfin 8.2 ta afka wa yankin Pacific, kusan kilomita 54 daga kudu maso yammacin birnin Pijijiapan.

An bayyana rahoton samun mummunar barna a jahohin Oaxaca da Chiapas.

Girgizar kasar, wacce ta afka wa birnin Mexico ranar Alhamis da misalin karfe 11:50 na dare agogon kasar, ta haddasa ruftawar gine-gine da dama yayin da muyane suka kwarara kan titunan birnin domin tsira da ransu.

Shugaba Peña Nieto ya ce wasu 'yan Mexico kusan miliyan 50 ne girgizar kasar za ta shafa, ana kuma tunanin samun karuwar wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan iftila'i.

Daga cikin wadanda suka mutu akwai a kalla mutum hudu a jihar Chiapas, da yara biyu a jahar Tabasco, da wani jariri daya da ya rasu sakamakon daukewar wutar lantarki ga na'urar da ke bashi numfashi.

Shugaban yankin Guatemala, ya ce mutum daya ya rasa ransa a yankinsa.

Yayin da aka bayar da rahoton mutuwar mutum 10 a jahar Oaxaca.

Wasu hotunan a shafukan sada zumunta na nuna yadda gine-gine suka rufta a jahar Oaxaca, tare da birnin Oaxaca wanda ke jahar Juchitan, inda nan ne fadar birnin da kuma mafiya yawan manyan ofisoshin gwamnati a yankin.

Rahotonnin da ke fitowa daga kafafen yada labaran kasar na cewa wani asibiti a jahar Juchitan ya rufta saboda iftila'in.

Hukumar dake gargadi kan Tsunami a yankin Pacific ta ce "girgizar kasar ta kai fiye da mita uku kusa da tekun Mexico" Ana ci gaba da aikin kwashe mutane a jahar Chiapas, inda aka ayyana dokar ta-baci.

Hukumar ta yi gargadin cewar za a iya samun barazanar tsunami a El Salvador, da Guatemala, da Honduras da kuma Costa Rica, sai dai ba za ta yi karfi sosai ba.

Sharhin wakilin BBC

Wannan Iftila'i ka iya tuno da wata mummunar girgizar kasa da aka yi a shekarar 1985 a birnin Mexico wadda ta haddasa mutuwar kusan a kalla mutum 10,000.

Girgizar kasar mai karfin maki 8.2 ta zarta karfin wacce ta faru a shekarar 1985 wacce ta afkawa ilahirin birnin na Mexico ta kuma hadda asarar dubban rayuka.

Wannan dai ita ce girgizar kasa mafi muni da aka fuskanata a wannan shekara a fadin duniya

Ga wasu daga cikin hotunan girgizar kasar

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Barnar da ta yi a jahar Oaxaca,
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wannan hoton wani gini kenan da ya rushe a garin Matias Romero na jahar Oaxaca

Labarai masu alaka

Karin bayani