Me ya sa 'yan gudun hijira ke komawa kiristoci?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Me ya sa 'yan gudun hijira ke komawa Kiristanci?

Dubban 'yan gudun hijirar Iran da ke neman mafaka a kasar Netherlands ne ke komawa addinin Kirista, inda da yawansu ke cewa suna barin addininsu ne don su samu dalilin da zai sa a ba su mafaka.

A yanzu hukumomin Netherlands suna yin tsauraran tambayoyi don gane ko masu shiga Kiristancin suna yi ne har cikin zuciyarsu ko don yaudara.

Amma ta yaya za su iya sanin ainihin abin da ke zuciyar mutanen?

Labarai masu alaka